BBC navigation

Chelsea na son sauya salon wasanta

An sabunta: 14 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 22:01 GMT
rigar chelsea

Rigar Chelsea

Attajirin nan mai kungiyar Chelsea Roman Abramovich ya zuba zunzurutun kudi har fam miliyan 65 domin bunkasa kungiyar ta yadda zata rinka wasan da zai kawatar tare kuma da samun nasara har ta dauki kofi.

Domin cimma wannan buri Abramovich ya dauko tsohon kocin kungiyar Andre Villas-Boas a kakar wasannin da ta wuce, koda ike kocin ya hau hanyar kawata wasan kungiyar amma rashin sa'ar cin wasanninsu ya sa aka sallameshi.

Bayan haka aka nada mataimakinsa Robero Di Matteo kocin riko, wanda nasarar da ya samu ta daukar kofin FA da na zakarun Turai aka bashi mukamin kocin na dun-dun-dun.

Hakan ya nuna gamsuwar attajirin da salon koyarda wasan kocin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.