BBC navigation

Garrincha kwarraren dan kwallon kafar da babu kamar sa

An sabunta: 15 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:18 GMT

Garrincha

Mafi yawanci mutane idan aka tambaye su ko wanene dan wasan kwallon kafar da ya fi kowa a Brazil, za su ambaci sunan Pele, wanda matsayinsa ya sa ya taka wata muhimmiyar rawa a bikin kamalla gasar Olympics ta Landan.

Amma wasu mutanen za su musanta haka da cewa Garrincha ne ya cancanci wannan matsayin, dan kwallon kafa dan baiwa da ya buga wa kasarsa wasanni 50 amma shaye-shaye ya jawo durkushewar tagomashinsa na kwallon kafa.

Ba abin mamaki ba ne kasancewar dansa Ulf Lindberg na daya daga cikin manyan masu goyon bayansa.

Ulf wanda shi ne dansa kwal namiji, an haife shi ne a shekara ta 1959 bayan dan kwallon ya nemi wata mace na gajeren lokaci a zuwan shi wani wasa a Sweden.

Duk da dai bai taba haduwa da mahaifinsa ba, yana tinkaho da cewa: “babu wani kamar Garrincha, yana da wani kayataccen salo na buga wasanni wanda duniya ba za ta manta da shi ba.”

Marubucin Tarihinsa, Ruy Castro ya bayyana dan wasan a matsayin cikakken matashin dan wasan da sana’ar kwallon kafa ta karbe shi.

A lokacin da Ulf yake wata tara da haihuwa mahifiyarsa ta bayar da shi riko ga wani iyali a Sweden.

Da ya cika shekara 9 sai iyayen rikon nashi suka bayyana mishi cewa shi dan Garrincha ne kuma yana da ‘yan uwa 14.

Ulf bai taba ganin mahaifinsa ba abinda ya sa ya ce: “ina bakin-cikin rashin haduwa da shi.”

A wannan makon, Ulf ya je Stockholm a matsayin bako na mussaman a wasan bankwana da Brazil za ta kara da Sweden a Rasunda, filin kwallon da mahaifinsa ya buga wasan karshe na wasan Kofin Duniya a shekara ta 1958, wanda a cikinsa ne Brazil ta lashe kofin farko a cikin kofuna 5 da kasar ta taba dauka.

Za a rusa filin kwallon ne amma har an gina makamanci sa a kusa da tsohon filin.

“Sau da yawa ina tunanin farincikin da zan samu da a ce na gamu da mahaifina kafin ya rasu saboda yadda yake burge ni.”

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.