BBC navigation

Robin Van Persie zai iya ci wa Manchester United kofi- Redknapp

An sabunta: 16 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:32 GMT
Robin Van Persie

Robin Van Persie

Tsohon manajan kulob din Tottenham Harry Redknapp ya ce, kwallayen da Van Persie zai iya ci wa kulob din Manchester United a Premier ka iya sa kulob din ya dau kofi.

Da komawar Van persie Manchester United, dan wasan tsakiyan kulob din Michael Carrick ya ce ya na sa ran cewa za su nanata nasarar da suka samu a baya ta daukan kofuna 3 a shekarar 1999.

Ranar Laraba Arsenal ta yadda da ta siyar da dan wasanta na gaba mai kwazo mai sekaru 29 dan asalin kasar Netherlands akan fan miliyan 24.

Redknapp ya shaida wa BBC cewa: “na hango wa Manchester United nasarar daukar kofi a kakar bana, tunda dai sun sayi Van Persie kuma zai iya kawo musu sauyi na mussamman saboda sun yi sa’a.”

Carrick ya kara da cewa: “in dai har abubuwa suka kankama mu abin farin ciki ne a garemu kuma muna masa maraba. Ya taka muhimmiyar rawa a kakar wasannin ta bara, kuma zuwan sa zai kara karfafa mana kulob.”

A kakar bara, Van Persie ya saka kwallaye 44 a raga a wasanni 57 da ya buga wa kasarsa da kuma kulob din sa, biyu daga ciki ma ya sa su ne a wasan da suka kara da Manchester United.

Kwantiraginsa a Arsenal zai kare ne a karshen kakar bana kuma ya bayyana cewa ba zai sabunta shi ba.

Dan wasan tsakiyar Manchester United na da, Lou Macari ya bayyana cewa duk wani dan wasa da ya doshi shekaru 30 kuma aka siye shi miliyoyin fama-famai wannan yana nuni ne ga duk wani mai niyyar cin kofi da ya yi damara

Macari ya ce: “Manchester United bata taba yin hakan ba duk da dai sun sayi Rooney da Ferdinand da tsada amma a lokacin suna matasa ne, tunda dai sun siye shi ina mai tabbaci da cewa za su dauki kofi a kakar nan.”

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.