BBC navigation

Arsenal da Barcelona sun cimma matsaya kan Song

An sabunta: 18 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:10 GMT

Dan wasa Alex Song yana kokawar karbe kwallo.

Dan wasan Arsenal Alex Song na dab da komawa Barcelona bayan kulob din biyu sun cimma matsaya a kan kudin da za a sayar da dan wasan.

Dan wasan tsakiyar mai shekaru 24 bai buga ba a wasan da kulob dinsa ya buga ranar Asabar da Sunderland inda aka tashi kunnen doki ba wanda ya jefa kwallo a raga.

Kocin Arsenal Arsene Wenger na shirin dauko aron dan wasan Real Madrid na tsakiya Nuri Sahin don ya maye gurbin Song.

Alex wanda ya ke da sauran shekaru biyu kafin kwangilar sa ta kare ya koma kulob din Arsenal ne daga kulob din Bastia na kasar Faransa a shekarar 2005.

Kocin Arsenaal dai na da kwarin gwuiwar cewa 'yan wasan da ya tanada domin kakar wasanni ta bana za su nuna bajinta ganin cewa Abou Diaby da Jack Wilshere da Tomas Rosicky na dab da dawowa wasanni bayan sun warke daga raunukansu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.