BBC navigation

'Man U ta fi kowacce kungiya damar lashe Premier'

An sabunta: 18 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:52 GMT

Roberto Mancini Manajan kungiyar Manchester City

Manajan Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Roberto Mancini, yace kungiyar Manchester United ce ke da alamun lashe gasar Premier ta wannan zangon wadda ake somawa ran Assabar.

Mancini yace wannan kuwa saboda kungiyar ce kawai ke da 'yan wasan gaba guda biyu da suka fi ko wadanni.

Manchester United dai ta sayo Robin Van Persie daga Arsenal kan kudi Fam miliyan 24 kuma zata hada shi ne da Wayne Rooney domin buga mata gaba.

Kungiyar Manchester City ce dai ta lashe kofin gasar a zangon wasannin da ya gabata bayan da ta saka kwallo biyu a ragar QPR a mintunan karshe na wasar da suka buga a ranar rufe gasar; abinda ya bata damar shan gaban United da yawan cin kwallaye.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.