BBC navigation

Buttner na shirin komawa United

An sabunta: 20 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 15:11 GMT
Buttner na shirin komawa United

United na fama da karancin 'yan wasan baya

Kulob din Manchester United ya cimma matsaya da kulob din Vitesse Arnhem a kan kudin da za ta biya don sayen Alexender Buttner, kuma tuni dan wasan ya isa Manchester don gwajin lafiya.

Dan wasan bayan mai shekaru 23, ya ce United ta yi ta zawarcinsa har tsawon wata guda, kuma sun kara nuna sha'awar su a 'yan kwanakin da suka gabata.

Da farko dai Buttner ya kusa komawa kulob din Southampton.

Ferguson dai ya shiga kasuwa ne don neman wanda zai yi zaman ko-ta-kwana ga Patrice Evra, bayanda ya bar Fabio ya tafi QPR a matsayin aro na shekara guda.

Buttner ya kan buga wa kasar sa ta Netherland wasa, ya shafe dukkan shekarun wasansa ne a Vitesse.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.