BBC navigation

Eduardo ya soki siyar da yan wasa da Arsenal ta yi

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:02 GMT
Tsohon dan wasan Arsenal Eduardo

Tsohon dan wasan Arsenal Eduardo

Babban kuskure Arsenal ta yi da ta siyar da Van Persie da Song, inji Eduardo.

Arsenan ta yi babban kuskure da ta siyar da Robin van Persie da Alex Song, to amma har yanzu ta na da damar yin nasara a wasannin kakar bana, kamar yadda tsohon dan wasan gaba na kulob din wato Eduardo ya fadi.

Su dai Van Persie da Song su ne manyan yan wasa na baya bayan nan da suka bar kulob din, wadda kofin da ta ci na karshe shi ne FA Cup a shekarar 2005.

A kakar wasa na bara dai, Arsenal ta zo ta ukku ne a gasar Premier, inda take kasa da maki 19 tsakaninta da zakarar wasan wato Manchester City da kulob din dake biye mata wato Manchester United.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.