BBC navigation

An kama dan wasan Arsenal bisa tukin ganganci

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:22 GMT
Andre Santos

Andre Santos

An kama dan wasan kulob din Arsenal bisa zarginsa da tukin ganganci, ana saura kwana guda a fara wasannin Premier na bana, kamar yadda yan sanda suka ce.

Yan sanda sun kama Andre Santos dan asalin kasar Brazil, mai shekaru 29 a duniya ne, a lokacinda suka hango shi ya na tukin ganganci, kuma da suka yi kokarin tsayar da shi, sai ya ki tsayawa.

Tuni dai aka sako Santos, wanda ya sha benci a wasan Arsenal na farko a kakar wasa na bana.

Yan sandan dai sun ce, ba a gwada nunfashinsa ko ya sha giya ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.