BBC navigation

Eto'o na gab da komawa cikin yan wasan Kamaru

An sabunta: 22 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:39 GMT
Samuel Eto'o

Samuel Eto'o

Samuel Eto'o zai koma doka wa kasarsa ta Kamaru wasa, bayan haramcin shiga wasanni na watanni takwas da aka sanya masa, ya cika.

An dakatar da Eto'o ne dan shekaru 31 a duniya, bayan yajin aikinda ya yi saboda rashin biyansa albashi a kulob din Marrakech.

Eto'o, wanda ya yi nasarar jefa kwallaye 54 ga kulob din Indomitable Lions, na sa ran shiga cikin tawagar yan wasan Kamaru guda 23 da za a bayyana a ranar Jumua mai zuwa.

Kamaru za ta buga wasanta na farko na shiga gasar cin kofin Afirka na shekarar 2013 a ranar 8 ga watan Satumba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.