BBC navigation

Fernando ya yi 'satar fage' - Cahill

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 10:51 GMT
Gary Cahill, mai tsaron gidan Chelsea

Gary Cahill, mai tsaron gidan Chelsea


Mai tsaron gidan Chelsea, Gary Cahill ya amince cewa kwallon da Fernando Torres ya zura a raga ka iya zama ta satar fage a taka ledar da kulob din ya yi da kulob din Reading a ranar Laraba.

Kulob din Chelsea ya doke Reading da ci hudu da biyu a wasan.

Torres ya karbi kwallo daga Ashley Cole, sannan ya zura ta a raga, abin da ya baiwa Chelsea damar shan gaban Reading da ci uku da biyu.

Amma shugaban kulob din Reading Brian McDermott ya dage cewa kwallon da dan wasan kasa da kasa na Sapaniya ya zura ta satar fage ce.

" Watakila ya dan yi satar fage, amma duk da haka mun zura kwallo". Inji Cahill.

Shugaban Chelsea ya kara da cewa " Sai dai abin ya yiwa Fernando kyau, tun da ya zura kwallaye biyu kuma yana wasa kamar yadda ya kamata."

McDermott ya tunkari mataimakin alkalin wasan bayan an hura usur din tashi, zuciyarsa na kuna yace mataimakin alkalin wasan ya yi kuskure.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.