BBC navigation

Saliyo ta dauki dan Najeriya ya buga mata wasa

An sabunta: 23 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:19 GMT

Tutar Kasar Saliyo

Kasar Saliyo ta saka sunan wani dan Najeriya a cikin jerin sunayen 'yan wasanda zasu buga mata wasar da zata yi da Tunisia ta neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa ranar takwas ga watan Satumba duk da cewar bai cika sharuddan hukumar FIFA na bugawa kasar wasa ba.

An dai saka sunan Victor Kayode ne a cikin jerin sunayen 'yan wasa19 bayan da ya nuna sha'awarsa ta bugawa Saliyo din wasa a watan Yuni.

Dan wasan mai shekaru ashirin da biyar yana buga wasane a kasar Azerbaijan kuma an saka sunansa cikin 'yan wasar kungiyar Leone star da za su fuskanci Tunisiya, amma ga alama bai cika ko daya daga sharuddan da Hukumar kwallon kafa ta duniya ta shimfidawa dan wasan da ke son komawa wata kasa da buga wasa ba.

Hukumar kwallon kafar Saliyo dai tace zata tuntubi hukumar ta FIFA domin sanin matsayinsa ga bugawa kasar wasa.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.