BBC navigation

Wigan ta amince da tayinda Chelsea tayi na sayen Moses

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:13 GMT

Dan wasa Victor Moses yana taka leda a cikin fili

Kungiyar Kwallo Kafa ta Wigan ta tabbatarda cewar ta amince da tayin da Chelsea tayi na sayen dan wasan ta Victor Moses.

Kungiyar hakama tace ta baiwa dan Najeriyar mai shekaru ashirin da biyu iznin tattaunawa da kungiyar wadda ke birnin London.

Wannan dai na zuwa ne a yayinda zangon saye da sayarda 'yan wasa ke kusantar makonsa na karshe a Ingila.

Chelsea dai na san ran cewa Moses zai buga mata wasa a gasar wasar shekara-shekara ta kulob-kulob din kasashen da suka lashe gasar zakarun Turai ranar Lahadi, inda za su kara da kulob din Manchester City.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.