BBC navigation

Chelsea ya sayi Victor Moses daga Wigan

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:46 GMT
Dan wasan kulob din Wigan Athletic, Victor Moses

Dan wasan kulob din Wigan Athletic, Victor Moses

Kulob din kwallon kafa na Chelsea ya sayi dan wasan Wigan Athletic a kan kudi fam miliyan tara.

A baya dai sau hudu Wigan na kin amincewa da tayin da Chelsea ya yi na sayen tsohon dan wasan Ingila na 'yan kasa da shekaru 21.

Wata sanarwar da kulob din Chelsea ya fitar ya bayyana cewa " Kulob din ya tabbatar da cewa bayan rashin nasarar sayen dan wasan sau hudu, yanzu a karo na biyar an cimma sharuddan sayen Victor Moses daga Wigan Athletic."

Chelsea zai biya fam miliyan bakwai nan take, daga bisani kuma kulob din zai biya ragowar fam miliyan biyu.

Wigan ta amince dan wasan Najeriyar na kasa da kasa ya yi magana da Chelsea.

Shugaban Wigan Roberto Martinez ya ce" Victor gwarzon matashi ne, kuma rawar ganin da ya nuna a ranar Lahadi ba kasafai ake samunta a tsakanin 'yan shekaru 21 ba."

Martinez na fatan sayar da wani dan wasa kafin lokacin musayar 'yan wasa ya kawo karshe a ranar 31 ga watan Agustar shekarar 2012.

Victor ya koma Wigan daga kulob din Crystal Palace a watan Janairun shekarar 2010 a kan kudi fam miliyan biyu da rabi.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.