BBC navigation

Manchester United ta kammala musayar 'yan wasa

An sabunta: 24 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 12:17 GMT
Shugaban kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson

Shugaban kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson

Shugaban kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce dan wasan gaba, Angelo Henriquez ne na karshe da kulob din zai siya a lokacin wasannin bazara.

Dan wasan dan kasar Chile mai shekaru 18 ya biyo bayan sayen dan wasan gaba Robin van Persie da 'yan wasan tsakiya Shinji Kagawa da Nick Powell da kuma mai tsaron baya Alexander Buttner zuwa Old Trafford.

Haka kuma Ferguson ya ce kulob din ba zai sayar da ko daya daga cikinsu ba, yayin da ake rade-radin sayar da Dimitar Berbatov.

" Tabbas ba za mu sake sayen wani dan wasa ba, haka kuma babu wanda za mu sayar" Inji Ferguson.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.