BBC navigation

Samuel Eto ba zai yi wa Cameroon wasa ba

An sabunta: 27 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 22:46 GMT

Samuel Eto

Dan kasar Cameroon Samuel Eto ya ce ba zai bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasar wasa ba saboda abin da ya kira rashin tsari na gari da kuma rashin gogewar masu kula da kungiyar.

Ya kamata Eto ya yi wasan da za a gwabza tsakanin Kasar Cameroon da kungiyar kwallon kafa ta kasar Cape Verde a watan Satumba na neman shiga gasar cin kofin Afrika, bayan ya kare watanni tawas da hukumomin kasa da kasa suka hana shi yin wasa.

Wasu masu nazari kan lamuran wasannin a kasar ta Cameroon sun ce ko da Eto ko babu Eto kasar za ta kai labari.

Sai dai har yanzu wasu na ganin kamata ya yi Eto ya halarci wannan wasan da zai gudana a watan Satumba.Wasu na ganin cewa rashiin halartar ta sa wata hanya ce ga matasan 'yan wasa na kasar ta Cameroon domin su nuna kwarewarsu a fagen wasanni.

A halin yanzu dai tana-kasa-tana-dabo tsakanin Eto da hukumar kwallon kafa ta Cameroon game da halartarsa wasa tsakanin kasar da Cape Verde.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.