BBC navigation

An kori Etoile ta Tunisia daga gasar zakarun Afrika

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 07:58 GMT
'Yan kungiyar kwallon kafa ta Tunisia

'Yan kungiyar kwallon kafa ta Tunisia

An kori kungiyar kwallon kafa ta kasar Tunisia, Etoile du Sahel daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika, bayan tashin hankalin da masoya kwallon kafa suka yi.

Tashin hankalin ya kai ga fasa taka ledar ta cikin gida tsakanin Etiole da Esperance a ranar 18 ga watan Agusta.

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ce ta dauki matakin a ranar Litinin, inda ta korar Etoile daga gasar ta kuma share sakamakon da kulob din ya samu nan take.

Wannan ne karon farko da aka taba korar wata kungiyar kwallon kafa a matakin tantance kungiyoyin da za su kara da juna.

Kulob din Esperance da SunShine Stars na Najeriya na da maki shida- shida, yayin da kulob din ASO Chief na Algeria ba shi da maki.

Saboda haka Esperance da SunShine Stars a yanzu sun samu shiga gungu na farko.

Masoya wasan kwallo sun shiga filin wasa har sau biyu, sai da ta kai 'yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa su.

Hakan ya faru ne a mintoci 69 da fara wasan, kuma Esparance ke da ci biyu, yayin da Etoile ke nema.

Yawanci a kasar ta Tunisia an fi yin wasannin kwallo ba tare da 'yan kallo ba tun bayan juyin-juya-hali, saboda tsoron tashin hankali daga 'yan kallo.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.