BBC navigation

Najeriya ta janye daga wasan sada zumunta da Masar

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:59 GMT
'yan wasan Super Eagles na Najeriya

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya

Najeriya ta janye daga karawar kwallon kafar sada zumunta da aka shirya gudanarwa tsakaninta da kasar Masar.

An dai shirya wasan ne da a ranar 11 ga watan Satumba mai zuwa a Hadaddiyar Daular Larabawa UAE.

Hukumar kwallon kafa ta kasar Masar ta yi shelar cewa tana tautauna da takwararta ta Najeriya kan wasar da ta shirya gudanarwa tsakanin kasashen biyu kwanaki uku bayan karawar da suka shirya yi da kasar Labariya don neman gurbi a gasar cin kofin nahiyar Afrika na shekarar 2013.

Mataimakin mai horar da kungiyar Pharaohs ta Masar, Diaa El-Sayed ya sanar a wata kafar labarai ta kasar Masar cewa, za su yi wasanin sada zumunta da kasashen Afrika ta Yamma da suka hada da Jamhuriyar Benin da kuma Najeriya a ranar 7 da 11 ga watan Satumba.

Sai dai kuma wani babban jami'in daga Najeriya ya shaida wa BBC cewa, sun dakatar da tattaunawa da Masar kan gudanar da wasan saboda hukumar kwallon kafa ta Najeriya ba ta lamunta ba da sahihancin shirye-shirye game da wannan wasan.

An dai sanar da 'yan wasan Super Eagles na Najeriya da jami'ansu game da soke wasa.

Najeriya da Masar sun gudanar da wasan sada zumunta a ranar 12 ga watan Aprilu a Dubai.

Kungiyar Pharaohs da ta kasance sau 7 zakaran Afrika ta sha Najeriya da ci 3 da 2.


Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.