BBC navigation

Dan Najeriya Kayode ba zai buga wa Saliyo wasa ba

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 19:58 GMT
Tutar Saliyo

Tutar Saliyo

Kasar Saliyo ta janye sunan Victor Igbekoyi Kayode dan Najeriya daga jerin 'yan wasan da za su taka mata leda.

Saliyon na shirin yin karon batar karfe ne a ranar 8 ga watan Satumba a Freetwon, tsakaninta da Tunisia a zagayen karshe na wasannin share fagen halarta cin kofin Afrika na shekarar 2013.

An dauki wannan mataki ne ganin cewa dan wasan bai cika sharudan hukumar kwallon kafa ta duniya ba wato FIFA.

Victor dan shekaru 25, ya je Saliyo bayan da mai horar da 'yan wasan Stars na Saliyo Lars Olof Mattsson ya gayyace shi ya zo daga Azerbaijan domin ya yi wasa a Saliyo.

Kakakin hukumar kwallon kafa ta Saliyo, Sorie Ibrahim Sesay shi ne ya sanar da sabon jerin sunayen 'yan wasa da za su bugawa Saliyo, sai dai kuma daga cikin sunaye 19 na 'yan wasa da ke taka leda a waje, sunan Victor Koyode kawai ne babu.

Koyode ya sanar da cewa, mamarsa ta shaida masa cewa kakansa daga bangaren babansa an haife shi ne a Saliyo. Kenan ya na da alaka da Saliyo, don shi ya sa yake son ya yi wa Saliyo wasa.

A cewar Sorie Ibrahim mai magana da yawun hukumar kula da wasanni ta kasar, labarin da BBC ta bayar game da daukar sa, shi ne ya hadasa rashin sa sunan Koyode a jerin sunayen 'yan wasan da za su taka wa Saliyo leda a wasan da za ta yi da Tunisia.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.