BBC navigation

Swansea na son a warware makomar Sinclair

An sabunta: 28 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 09:09 GMT
Scott Sinclair

Scott Sinclair

Shugaban kulob din Swansea City, Huw Jenkins na son a warware makomar dan wasa, Scott Sinclair da Manchester City kafin a rufe musayar 'yan wasa.

Dan wasan gefen bai shiga cikin tawagar Swansea ba, a karawar da kulob din ya yi da West Ham a ranar Asabar, kuma ya shaidawa kulob din shi ba zai sanya hannu a wani sabon kwantiragi ba.

Rahotanni sun ce Swansea ta amince da wata yarjejeniya tsakanin ta da Man City.

Amma Jenkins ya ce " A gaskiya ba mu cimma wata yarjejeniya a halin yanzu da Man City ba."

" Ina tunanin idan da da gaske suke game da Scott Sinclair da sun yi magana mai karfi fiye da wadda suka yi, amma wannan su ya shafa." Inji Jenkins.

Inda ya kara da cewa " An yi ta jan maganar sosai, kuma ina fatan za a kammala ta a cikin 'yan kwanaki masu zuwa."

Wani dan wasan kuma da zai bar Swansea kafin rufe musayar 'yan wasa a ranar juma'a mai zuwa, shi ne Garry Monk wanda ake batun zai koma Bristol City.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.