BBC navigation

Fulham ta sayi dan wasan Man United Dimitar Berbatov

An sabunta: 31 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 18:29 GMT
Dmitar berbatov

Kungiyar kwallon kafa ta Fulham ta kulla yarjejeniyar shekaru biyu da dan wasan gaba na Man United Dimitar Berbatov.

Dimitar Berbatov dan kasar Bulgaria yana da shekaru 31 a duniya, kuma kulob-kulob da dama sun yi zawarcinsa ciki har da Fiorentina da Juventus na kasar Italiya, amma ya zabi ci gaba da zama a gasar Firimiya ta Ingila.

Fulham dai ba ta bayyana ko nawa ta sayo dan wasan ba.

Shi dai dan wasan ya ce : " Tun da Fulham ta tuntube shi ya yanke shawarar zuwa yi wa kungiyar wasa."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.