BBC navigation

Za a haramtawa Eto'o buga kwallo a rayuwarsa

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 08:27 GMT
Dan wasan Kamaru, Samuel Eto'o

Dan wasan Kamaru, Samuel Eto'o


Dan wasan kasa da kasa kuma dan Kamaru Sameul Eto'o ka iya fuskantar haramcin buga kwallo a tsawon rayuwarsa, idan ya ki bugawa kasarsa wasa.

Mai magana da yawun hukumar kwallon kafa ta Kamaru, Junior Binyam ne bayyana hakan.

An dai zabi dan wasan gaban a tawagar Kamaru da za ta kara da Cape Verde, a zagayen karshe na neman shiga gasar zakarun nahiyar Afrika na 2013 wanda za a yi a watan Satumba mai zuwa.

Sai dai Eto'o ya janye daga bugawa kasarsa wasan bisa dalilan da ya kira rashin sanin makamar buga wasa da kuma almubazzaranci wajen tafi da al'amuran kungiyar kwallon kafar.

An dakatar da Eto'o na watanni takwas saboda yajin aikin da yayi a Marrakech, kuma har yanzu yana kan matsayinsa kan batutuwan da yake ganin ba a warware su ba.

Amma Binyam ya shaidawa BBC cewa " Dukkan dan wasan da aka neme shi a kasarsu to ya zama dole ya zo ya taka leda, dan wasan ba shi da wani zabi."

Ya kara da cewa " A dokar ladaftarwa ta kungiyar Kamaru za a iya dakatar da dan wasa, kuma dakatarwar za ta shafi kulob dinsa."

" Haka kuma za a iya haramta masa buga kwallo a fadin rayuwarsa, idan bai halarci kiran da aka yi masa zuwa sansani ba. " Inji Binyam.

Jamhuriyar Kamaru ta kira Leonard Kweuke don maye gurbin Eto'o a karawar da za a yi a ranar 8 ga watan Satumba mai zuwa.

Binyam ya kuma bayyana cewa hukumar ta maida hankali a kan shirya kungiyar kwallon kafar, amma za ta dauki matakan ladaftarwa daga bisani.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.