BBC navigation

Ga alama Walcott ba zai bar Arsenal ba a bana

An sabunta: 29 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 17:06 GMT

Walcott yana murnar jefa kwallo a raga

Ga alama dan wasan gaba na Arsenal Theo Walcott ya shirya cigaba da kasancewa a kulob din a wannan zangon na wasanni da ake ciki bayan wata tattaunawar lumana da suka yi da Koch Arsene Wengar ranar Laraba.

Kwantaragin dan wasan mai shekaru 23 za ta kare ne a 2013 kuma har yanzu bai saka hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar ba.

An dai yi ta rade-radin cewar zai yiwu ya bar kulod din, inda har Manchester City ta kasance cikin kungiyoyin da suka rika zawarcinsa.

Dan wasan na kasar Ingila ya gana da Wenger ne bayan 'yan wasan Arsenal sun gama karbar horo ranar Laraba; bayan da ta bayyana cewar dan wasan ya ki karbar tayin wani kwantiragin shekaru biyar inda zai rika karbar Fam 75,000 a mako.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.