BBC navigation

Paralympics: Birtaniya ta samu lambar girma ta farko

An sabunta: 30 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 16:27 GMT

Lambar zinare ta gasar Paralympics

Tawagar Birtaniya a gasar Olympics ta masu nakasa da akeyi a London, ta lashe lambar girmanta ta farko a ranar farko ta soma gasar.

Mai tseren keke Mark Colbourne ya lashe lambar azurfa a tseren kilomita daya na maza a filin Olympics Park ranar Alhamis.

A wasannin Olympics 'yan tseren Birtaniya Jonathan Fox da Sarah Storey sun kafa tarihi makamancin wannan da lashe lambobin girma kafin kasar China ta samu lambar zinare ta farko a gasar.

A ranar farko ta gasar ta Paralympics, masu shirya gasar na son mayar da hankali ne kan gundarin wasannin ba wasu batutuwan da ke zagaye da su ba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.