BBC navigation

Guti ya soki Mourinho saboda sayen Essien

An sabunta: 2 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 14:16 GMT

Guti

Tsohon dan wasan Real Madrid, Guti, ya soki kocin kulob din, Jose Mourinho, saboda sayar da Esteban Granero da ya yi da kuma aron Michael Essien.

Guti, wanda ya bugawa kulob din wasannin La Liga sau 350 tsakanin shekarar 1995 da 2010, ya bayyana fushinsa a kan matakin da Mourinho ya dauka na maye gurbin Granero da dan wasan Chelsea, Essien.

"Akwai abubuwan da bana fahimta a game da kwallon kafa; daya daga cikinsu shi ne yadda za a bar Granero ya tafi sannan Essien ya zo kulob din. Granero yafi kwarewa a wasa, kuma shi dan Spain ne," Guti ya sahidawa jaridar Marca.

Ya kara da cewa: "A yanzu haka 'yan wasan da suka fi kwarewa 'yan Spain ne. Abin da ke faruwa shi ne, ana kashe makudan kudi kafin a sayo 'yan wasan kasashen waje; hakan na matukar bata mini rai''.

Granero ya koma kulob din Queens Park Rangers, inda ya buga musu wasa a gasar zakarun Turai da suka yi da Manchester City a filin wasa na Etihad ranar Asabar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.