BBC navigation

Paralympics: Shugaba ba zai shaidi bikin rufewa ba

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:40 GMT

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta nakasassu na duniya Jacques Rogge

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta nakasassu na duniya Jacques Rogge ba zai samu halartar bikin rufe gasar ta bana wadda ke gudana a birnin London ba.

Mai magana da yawun kwamitin ya fada ranar talata cewa za a yiwa Jacques Rogge aikin tiyata a katara a wannan makon kuma zai bukaci kwanakki kafin ya warke.

Rogge dan kasar Belgium mai shekaru saba'in dai ya shaidi bikin bude gasar ranar laraba.

Sai dai ba zai shaidi biki mai matukar kayatarwar da aka shirya domin rufe gasar ta tsawon kwanakki 11 ba a ranar lahadi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.