BBC navigation

Pistorius ya tsira daga ladabtarwa

An sabunta: 4 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:42 GMT

Dan tsere guragu Oscar Pistorius

Kwamitin shirya gasar Olympics ta nakasassu (IPC) yace ba bu wani matakin ladabatarwa da za a dauka kan Oscar Pisterious saboda sukar da yiwa kwamitin ranar litinin.

Dan tseren guragun na kasar Afrika ta kudu mai shekaru 25 ya soki kwamitin kan ka'idodinda ya gindaya dangane da tsawon kafafuwan karfenda guragu ke anfani dasu wajen tsere bayan dan kasar Brazil Allan Oliviera ya doke shi.

Mr Pistorus yayi kakkausar suka da yadda gasar wasan ta kasance, yana mai cewar masu shirya gasar ta Paralympics na bukatar su duba lamarin da kuma abubuwan da dokar gasar wasannin ta tanada; amma sai Kwamitin na IPC ya nace kan cewar an riga an gwada tsayin kafafuwan,kuma babu batun keta hakkin dokar wasannin.

Daga baya dai Pisterious ya nemi afuwa kan kalamanda yayi da kuma lokacin da ya yi su abinda ya sa yanzu daraktan sadarwa na kwamitin Craig Spence yace ba za a ladabatarda shi ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.