BBC navigation

Andy Carroll ya samu sagewar kafa

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:41 GMT
Andy Carroll

Andy Carroll

Dan wasan gaba na kulob din West Ham, Andy Carroll ba zai buga wasa ba na tsawon makonni biyar zuwa shida saboda sagewar kafa.

Dan wasan dan shekaru 23 ya fice daga taka leda tsakanin Moldova da Ukraine, a gasar share fagen cin kofin duniya ta nahiyar Turai.

Hoton da aka dauka na sharabarsa ya nuna cewa Carroll ya samu mummunan sagewa, abin da yasa a ka cire tsammanin zai bugawa kulob dinsa na West Ham wasanni hudu.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne, Hammers ta karbi aron Carroll daga Loverpool.

Mai horar da 'yan wasan kulob din West Ham, Sam Allardyce ya ce " Dan wasan zai dauki wani lokaci yana jinya."

Inda ya kara da cewa " Sam bai ji dadi ba lokacin da ya samu raunin domin hakan na nufin ba za shi Ingila ba, kuma inda yake son zuwa kenan."

Sai dai ya kara da cewa kulob din na fatan bayan Carroll ya warke zai cigaba da taka leda a duk mako, tare da zura kwallaye a ragar abokan karawarsu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.