BBC navigation

Nijar ta nada Gernot Rohr a matsayin sabon koci

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:03 GMT

Gernot Rohr sabon Kocin Nijar

Jamhuriyyar Nijar ta nada Gernot Rohr a matsayin sabon mai horar da kungiyar 'yan wasan kasar.

Dan kasar Jamus din zai kama jan ragamar kungiyar kwallon kafar Nijar a ranar Lahadi mai zuwa.

Kuma zai tafi da kungiyar zuwa Guinea a zagayen karshe na wasan share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar 2013.

Rohr wanda ya maye gurbin dan kasar Faransa, Rolland Courbis, ya taba zama mai taimakawa mai horar da 'yan wasan Gabon a zagayen kashe na gasar cin kofin nahiyar Afrika a farkon shekarar 2012.

Sai dai bayan an fitar ga Gabon a zagayen na kusa da na kusa da na karshe, kasar bata sabunta kwantiraginsa ba.

Rohr mai shekaru 59 ya taba bugawa Bayern Munich da Girondins Bordeaux wasa, kuma ya horar da 'yan wasan kulob din Bordeaux a lokacin da Bayern ta lallasa Bordeaux a gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 1996.

Amma kawo yanzu hukumar kwallon kafa ta Nijar bata fitar da bayani game da kwantiragin nasa ba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.