BBC navigation

An amince da tafiyar Owen zuwa Stoke City

An sabunta: 5 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:50 GMT

Sabon dan wasan Stoke Michael Owen

Hukumar shiryar gasar Premier League ta amince da tafiyar Micheal Owen zuwa kulod din stoke city.

Tsohon dan wasan gaban na Manchester United da Liverpool da kuma Ingila ya sanya hannu ne kan wani kwataragin shekara daya da kungiyar ranar talata.

Sai dai dole sai da Stoke ta jira amincewar hukumar kafin ta saka dan wasan mai shekaru 32 a cikin jerin sunayen 'yan wasa 25 da za su buga mata gasar a wannan zangon.

Bayan da hukumar ta sanarda amincewar ta a ranar laraba, Owen ya rubuta a shafinsa na twitter cewar ''...Ta tabbata. A yanzu ni dan wasan Stoke ne.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.