BBC navigation

Kano Pillars ce zakarar premier League

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:42 GMT

Aminu Maigari, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya

Za a nada kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillar a zaman zakarrun gasar Premier League ta Najeriya ranar Jumu'a, bayanda hukumar da ke shirya gasar NPL ta kori Ocean boys daga gasar saboda kin buga wasanni biyu a jere.

Sakamakon korar kungiyar ta jahar Bayelsa ranar laraba, an ciccire dukkanin maki-makinda kungiyoyi suka samu daga buga wasa da ita a duk tsawon wannan zangon.

Kungiyar ta Pillars wadda aka fara nadawa zakara a shekarar 2008 za ta fi kowacce cin moriyar hukumcinda aka yiwa Ocean Boys din, saboda hakan ya bata damar cigaba da kasancewa ta daya da maki 60, bayanda aka cire maki hudu da ta samu daga buga wasa da kungiyar ta jahar Bayelsa.

Saboda haka wasan karshenda za ta buga da Sunshine stars a ranar jumu'ar zai kasance na cika ka'ida kawai domin ko ta yi nasara ko bata yi ba ita ce za ta zamo zakara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.