BBC navigation

Oscar Pistorius ya samu lambar Zinare

An sabunta: 6 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 08:04 GMT
Oscar Pistorius

Oscar Pistorius

Dan wasan nakasassu na Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius ya samu lambar zinarensa ta farko a gasar Olympics ta nakasassu ta shekarar 2012.

Hakan ya biyo bayan lashe gasar tseren yada kanin wani na mitoci 100.

Tawagar Afrika ta kudu ta kafa sabon tarihi, inda ta lashe gasar cikin mintuna 41 da dakikoki 87.

Kasar Brazil da kuma Amurka mai kare kanbunta sun turza, amma kuma an fitar da su daga gasar, abin da ya sa China da Jamus suka dauki lambobin Azurfa da Tagulla.

Tun da fari dai Pistorius wanda ke kare kambunsa a tseren mitoci 100, ya samu nasarar shiga gasar da za ayi yau Alhamis.

A ranar Laraba ne karon farko da dan wasan dan shekaru 25 ya fito filin wasa tun kayen da ya sha a ranar Lahadi a tseren mitoci 200.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.