BBC navigation

An rufe gasar Paralympics da kasaitaccen biki

An sabunta: 9 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:35 GMT

Bukin rufe gasar Paralympics

An gudanarda bikin rufe gasar Olympics ta nakasassu watau Paralympics da daren ranar lahadi a birnin London da wani kasaitaccen biki da masu shirya shi suka kira bukin wuta.

Wadanda suka shirya shi sun ce bukin wani bankwana ne mai sosa rai ga abinda suka baiyyana da gasa mafi samun nasara a tarihin gasar ta guragu wato Paralympics.

Fiye da 'yan wasa nakasassu 4,250 daga kasashe 164 ne suka fafata a gasar inda aka kafa sabbin bajinta har 250.

Kusan tikitin shiga filin wasa miliyan uku ne aka saida a cikin kwanannki goma sha dayan da aka kwashe ana gudanarda gasar.

Wasanninda aka gudanar a gasar sun kawo karshen ne da wasar karshe ta kwallon kafa inda Rasha ta dauki lambar zinare bayan doke Ukraine da ci 1-0.

Tawagar makadan Birtaniya da ake kira ColdPlay ce suka jagoranci bukin wanda ya soma da karfe 8:30 na daren jiyan agogon Burtaniya inda makada daban-daban suka sheke ayar su.

Da somawar bukin sai da aka yi jinjinar bangirma ga wata kungiyar bayarda agaji ta soji da ake kira 'Help for Heroes' da kuma wasu jami'an sojin kasar da suka samarda tsaro a lokacin gasar.

A koluwar bikin dai an kashe fitilllun da suka haskaka filin wasannin inda kuma aka mika tutar karbar bakuncin gasar ga birnin Rio de jeneiro na Brazil wanda zai shirya gasar ta gaba a shekara ta 2016

Magajin garin Birnin London ne ya mika tutar ga Shugaban kwamitin paralympics na duniya wanda shi kuwa ya mika ta ga magajin garin birnin Rio de Janeiro.

An dai watse daga gasar ta paralympics ta 2012 ne kasar China na kan gaba a jerin kasashen suka samu lambobin yabo a gasar da samun lambobi 231 sai kuma Rasha ta biyu da lambobi 102 yayinda Burtanita mai masaukin bakin ke da lambobi 120. Rasha dai tasha gaban ta ne saboda ta fita lambobin zinare.

Daga cikin kasashen Afrika da suka shiga gasar dai kasar Tunisia ce ta farko wadda ke matsayin ta 14 a matakin duniya da lambobin 19 , Sannan Afika ta kudu ta biyu da lambobi 29 inda ta zo ta 18 a matakin duniya, sa 'annan kuma Najeriya ta ukku da lambobi goma 13 inda ta zo ta 22 a matakin duniya.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.