BBC navigation

Serena Williams ta lashe gasar US Open

An sabunta: 10 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 09:28 GMT
Serena Williams

Serena Williams


'Yar wasan kwallon Tennis Ba Amurkiya, Serena Williams ta doke Victoria Azarenka, inda ta lashe gasar Tennis ta US Open a karo na hudu.

'Yar wasan mai shekaru 30 ta ci galabar ne a wasan da suka kara a filin wasa na Arthur dake Amurka.

Kodayake 'yar wasan Tennis mace ta farko a duniya wato Azarenka ta yi kokari a gasar, amma Serena ta lallasa ta, abin da ya sa kuma ta lashe gasar.

Serena ta kasance mace ta farko wacce ta haura shekaru 30 da ta taba daukar kofi a gasar Tennis na US Open, tun lokacin da Martina Navratilova ta lashe gasar a shekarar 1987.

"Sam ban yi tsammanin zan lashe gasar ba, domin har na fara shirya jawabin da zan yi a matsayin ta biyu a gasar, saboda yadda Azarenka ta nuna kwazo a wasan." Inji Serena.

Azarenka ta yi kuka domin bata cika burinta na zama 'yar kasar Belerus ta farko mace da ta taba daukar kofin gasar ta US Open ba.

Sai dai ta bayyana cewa " Mun fafata sosai, amma Serena ta cancanci ta lashe gasar, ta nuna cewa lallai ita kwararriya ce."

'Yar wasan 'yar shekaru 23 ta kara da cewa " An girmama ni ta hanyar tsayawa tare da jaruma, zan fita daga filin wasannan ba tare da da-na-sani ba. "

Nasarar da Serena ta samu ya zo shekaru 13 bayan samun nasararta a karo na farko a gasar mata tilo dake karawa da juna a gasar Tennis ta US open.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.