BBC navigation

Uefa ta sanya takunkumi a kan kulob-kulob 23

An sabunta: 11 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:01 GMT
Shugaban Uefa, Michel Platini

Shugaban Uefa, Michel Platini

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa ta sanya takunkumin farko na dakatar da bada kudi ga kungiyoyin kwallon kafa 23 da suka ki bin dokokinta.

Kungiyar da ta lashe gasar Europa league wato Atletico Madrid da Malaga da Sporting da kuma Fenerbahce na daga cikin kulob-kulob din da ake bincike.

Kungiyoyin kwallon kafar na fuskantar bincike ne, saboda rashin biyan kudade ga wasu kulob-kulob din, ko ga ma'aikata ko kuma rashin biyan haraji ga hukumomi a kan lokaci.

Hukumar ta Uefa ta sanya dokokin ne, saboda ta tursasa wa kungiyoyin kwallon kafa su bi da al'amuransu daidai-ruwa-daidai-tsaki.

An dai baiwa kulob-kulob din 23 wa'adin zuwa 30 ga watan Satumba, su gamsar da Uefa cewa ba su da matsalar kudade.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.