BBC navigation

Hillsborough: Firai ministan Birtaniya ya nemi gafara

An sabunta: 12 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:20 GMT
David Cameron firai ministan Birtaniya

David Cameron firai ministan Birtaniya


Firai ministan Birtaniya, David Cameron ya nemi gafara game da abin da ya kira rashin adalci biyu a bala'in da ya auku a Hillsborough.

Yayin da yake magana bayanr fitar da wani rahoto mai zaman kansa a kan wasu takardu da ba a san da su ba a baya game da bala'in.

Ya ce " 'Yan sanda sun gaza wajen yin abin da ya kamata kuma sun yi kokarin dora laifin a kan masoya kulob din Liverpool.

Masoya wasan kwallon kafa 96 ne suka mutu, bayan an tattake su a Sheffield a shekarar 1989.

Haka kuma shi ma editan jaridar Sun da ta wallafa labarin tana dora laifin a kan masoya wasan kwallon, Kelvin Mackenzie, shi ma ya bada hakuri game da abin da labarin da suka wallafa.

Mr. Cameron ya shaidawa 'yan majalisa cewa, da masu aiyyukan ceto sun kai dauki cikin hanzari da an ceto rayukan mutane da dama.

Shugaban kulob din Liverpool, Tom Werner ya ce " A yau duniya ta ji gaskiyar abin da ya faru a Hillsborough."

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.