BBC navigation

Kulab din Kurket na Ingila ya lallasa Australia

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:58 GMT

tawagar Yan wasan Kurket na Ingila

Kungiyar Kulab din Ingila ta kwallon Kurket sun lallasa takwarorin su na Australia da ci tara a wani wasan share fage a Colombo don tunkarar gasar

Twenty 20 ta Duniya wadda za a fara a yau Talata.

Kulab din wanda yake rike da kambun gasar ta Duniya ya samu sakamakon kwallo dari da saba'in da biyu takwarorin su kuma na Australia sun samu shida.

Alex Hales ne ya fi kowa zura kwallayen inda ya ci hamsin da biyu.

Wannan ne karo na biyar da Kungiyar kwallon Kurket ta Ingilar ta samu nasara kan Australia a wannan shekarar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.