BBC navigation

Rangers za ta yi rashin Johnson a kakar bana

An sabunta: 17 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:54 GMT

Queens Park Rangers

Dan gaban kungiyar kwallon kafa ta Queens Park Rangers Andy Johnson zai iya rasa samun damar buga sauran wasannin wannan kakar bana bayan wani rauni da yake fama da shi.

Dan wasan mai shekaru talatin da daya ya dage kafar sa a mintina talatin da biyu na wasan da aka yi ranar Asabar da aka tashi cancarasa tsakanin Queens Park Rangers din da kuma Chelsea.

Johnson dai ya bayyana sau hudu ke nan tun bayan da akayi musayar sa ya koma kulab din daga Fulham.

Kochiyan kulab din Mark Hughes yana da sauran 'yan wasan gaba masu kai farmaki kamar su: Bobby Zamora, jamie Mackie da kuma Djibril Cisse.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.