BBC navigation

Patrice Evra ya shirya buga wasan Man U

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:05 GMT

Patrice Evra

Dan wasan Manchester United Patrice Evra ya shirya tsaf don buga wasan farko na gasar champions League wanda za su kara da Galatasaray, bayan sauki da ya samu daga wani rauni da ya ji.

Dan wasan mai shekaru talatin da daya ya ji rauni ne karami abun da ya hana shi buga wasan kulab din da Wigan inda Manchester United din ta yi nasara kan Wigan din.

Dan wasan gaban nan Robin Van Persie wanda ya shigo a zagaye na biyu a wasan ranar Asabar da ta gabata da kuma dan kasar Japan Shinji Kagawa su ma sun yi horo na shirin wasan.

Darren Fletcher wanda bai yi wasa ba tun watan Nuwamban shekara ta dubu biyu da goma sha daya zai dawo wasan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.