BBC navigation

Manchester United ta samu ribar £23.3m

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 17:09 GMT

Yan wasan Manchester United

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta samu ribar Pam miliyan ashirin da uku da digo uku a wani sabon rahoto da ta futar a wannan shekarar.

Ribar dai ta kai kaso saba'in da tara da digo biyu cikin dari.

Wannan ribar ita ce mafi girma tun lokacin da kulab din ya shiga hannayen jari na birnin New York a watan da ya gabata.

An sanya hannayen jarin kulab din a ranar goma ga watan Agusta kan dala goma sha hudu ko wacce, amma dai tuni ta fado kasa.

Rancen da kulab din yake yi ya ragu matuka a wannan shekarar daga Pam miliyan dari hudu da hamsin da tara zuwa Pam miliyan dari hudu da talatin da bakwai; abin da yake da mahimmanci ga masu son kulab din da kuma masu saka hannun jari.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.