BBC navigation

Mourinho, Mancini na son City ta ci kofin champions league

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 10:22 GMT
Mai horar da 'yan wasan Real Madrid, Jose Mourinho

Mai horar da 'yan wasan Real Madrid, Jose Mourinho

Mai horar da 'yan wasan kulob din Real Madrid, Jose Mourinho ya yi imanin cewa kulob din Manchester City zai dauki kofin gasar Champions League ko ba-dade ko ba-jima.

Mourinho ya ce " Da ganin yadda kulob din na Man City ke wasa, ka san wata rana za su dauki babban kofi"

Yayin da yake magana gabannin wani taro da za a yi yau Talata a Madrid, mai horar da 'yan wasan kulob din Manchester City, Roberto Mancini ya amince cewa, wani lokaci a nan gaba kulob dinsa zai dauki kofin gasar.

Mancini ya bayyana cewa " Na tabbatar wata rana za mu dauki kofin a nan gaba."

Tsoshon mai horar da 'yan wasan kulob din Chelsea, Mourinho ya ciwo wa kulob din kofuna biyu a gasar premier league, sai dai bai ciwo wa Chelsea kofi a gasar Champions League ba.

Amma a lokacin da ya ke kulob din Porto da Kuma Inter Milan ya ciwo wa Kulob din biyu kofin na Champions League.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.