BBC navigation

Villas-Boas na son Tottenham ta ci kofin Turai

An sabunta: 18 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:39 GMT

Andre Villas-Boas

Kochiyan kulab din Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Andre Villas-Boas ya zaburar da 'yan wasansa kan su ci kofin Nahiyar Turai a wannan kakar bana.

Kochiyan ya ce ya zama wajibi 'yan wasan su yi wani abu mai mahimmanci kan gasar.

A baya baya dai Kulab din sun samu nasarar cin gasar a alif dari tara da tamanin da hudu lokacin da suka doke Anderlecht a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Andre ya ce aiki ne ja, ya kara da cewa dole ne kulab din yaci wasannni goma sha biyar kafin ya je wasan karshe a gasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.