BBC navigation

Di Matteo bai ji dadin kunnen doki da Juventus ba

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 07:59 GMT
Roberto Di Matteo

Roberto Di Matteo

Mai horar da 'yan wasan Chelsea, Roberto Di Matteo ya ce kulob din bai ji dadi ba matuka, bayan ya bada kai bori ya hau a karawarsu da Juventus.

Taka ledar ta sa Juventus ta wuce Chelsea da kwallaye biyu a gasar Champions League.

Sai dai Di Matteo ya yaba wa Oscar wanda ya zura kwallaye biyu a ragar Juventus, a ranar ta farko da ya fara wasa.

Dan wasan ya zura kwallayen a cikin mintoci biyu, kafin Juventus ta farke ana saura mintoci goma a tashi.

Di Matteo wanda ya jagoranci Chelsea har ta dauki kofinta na farko a gasar Champions League a bara, ya kara da cewa " Oscar ya yi kyakkyawar fitowa. "

Dan wasan tsakiyar mai shekaru 21 ya dauki wani lokaci yana tare da tawagar kasarsa ta Brazil, kafin dawowarsa Chelsea, abin da ya sa Di Matteo ke ganin yana bukatar karin horo.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.