BBC navigation

Kochiyan Liverpool ya ajiye gogaggun 'yan wasa

An sabunta: 20 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:43 GMT

Kochiyan Liverpool, Brendan Rodgers

Kochiyan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Brendan Rodgers ba zai tafi da wasu gogaggun 'yan wasansa kasar Sweden ba, inda kulob din zai kara da Young Boys a gasar Europa ranar Alhamis.

Daga cikin 'yan wasan da ba za su buga wasan ba akwai Steven Gerrard da Luis Suarez, da Pepe Reina da kuma Joe Allen.

Rodgers, ya ce ya yi hakan ne don ya tafi da 'yan wasa matasa wadanda yana ganin za su iya bada wata gudummawa.

Ya kara da cewa babban dalilin kuma na daukar matakin shi ne ya rage yawan masu tafiyar kuma ya bawa wasu 'yan wasa kwarin gwiwar cewa suma suna da dama.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.