BBC navigation

Drogba ya bayyana farin cikinsa da komawa Shanghai

An sabunta: 21 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 16:35 GMT
drogba

Drogba

Didier Drogba ya hakikance cewa lallai ya ji dadin kasancewa a China, tare da bayyana cewa zai iya bakin kokarin sa don ganin ya kammala kwantiraginsa na tsawon shekara biyu da rabi a kulub din Shanghai Shenhua.

Dan kimanin shekaru 34, dan wasan ya bar kulub din Chelsea ne kafin ya koma Shanghai.

Rahotannin da aka bayyana da suka nuna cewa, kulub din na Shanghai na fuskantar matsalar kudi, sun sanya shakku kan makomar dan wasan dan asalin Ivory coast kan ina zai nufa, lamarin da ya sa aka rika hasashen zai koma Premier Ingila.

Sai dai kuma Drogba ya shaidawa BBC cewa, zai kasance a China har sai wa'adin kwantiraginsa ya kare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.