BBC navigation

An tuna da wadanda suka mutu a Hillsborough

An sabunta: 23 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:36 GMT

Liverpool Hillsborough

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da Manchester United sun yi bikin tunawa da wadanda suka rasu a annobar Hillsborough kafin su yi wasan su na Premier League ranar lahadi.

Wasan dai shine karo na farko da akayi a filin wasa na Anfield tun bayan rahoton da kwamiti mai zaman kansa ya futar kan abin da ya gano a binciken annobar da ta afku a wasan kusa da karshe na Kofin FA a shekarar alif dari tara da tamanin da tara.

Kwamitin dai ya wanke masu son kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da zargin da ake musu.

An dai tuna wadanda suka mutu din da fulawowi da rubobin balu kafin a fara wasan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.