BBC navigation

Hukumomin Kamaru na rokon Eto'o ya dawo

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 19:53 GMT
samuel eto'o

Samuel Eto'o

Manyan masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni a kamaru sun gana da Samuel Eto'o a kokarin shawo kan dan wasan domin ya sauya shawarar da ya yanke ta daina bugawa kasarsa wasa.

Eto'o wanda ke yi wa kungiyar Anzhi Makhachkala ya ki bugawa Kamaru wasa tun bayan da ya kammala wa'adin dakatarwar watanni 8 a kan rawar da ya taka ta yajin wasan da 'yanwasan kasar suka yi a bara.

Tun daga sannan ne Eto'o wanda ya kira shugabannin hukumar kwallon kafa ta kasar 'yandagaji da ba su da kwarewar gudanar da aiki ya kuma juyawa kasar baya wajen yi mata wasa.

Sakamakon ganawar da Praiministan kasar Philemon Yang da ministan wasanni Adoum Garoua da da manaja da kuma kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar suka yi da danwasan a ranar Litinin ana sa ran zai sauya shawara amma da wasu sharudda.

A cikin makon nan ne kocin kasar Jean Paul Akono zai bayyana sunayen 'yanwasan da zasu buga wasan karo na biyu na neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika da Cape Verde wanda a karon farko Kamarun ta sha kashi da ci biyu ba ko daya, wanda hakan kuma ya jefata cikin hadarin kasa zuwa gasar cin kofin karo na biyu a jere.

Yanzu dai ba a tabbatar ko danwasan zai zama cikin wadanda zasu buga wasan ba ko a'a.

Zakaran wasan kwallon zunguren sanda a tebur Snooker na duniya Ronnie O’sullivan ya sami koma baya inda ya yo kasa daga cikin jerin gwanayen wasan na duniya 16.

O’sullivan ya ci bayan ne a karon farko tsawan shekaru 19 bayan da ya sami shiga wannan sahu.

Zakaran wanda yanzu yake mataki na 17 a duniya ya gamu da wannan matsala ce saboda kin da ya yi na ya kulla kwantiragi ta danwasa a watan Yuni amma bayan makwanni 8 ya mika wuya wanda kuma hakan ya bashi dammar sake dawowa fagen wasan a watan nan amma na jeri na 76 a duniya Simon Bedford ya yi nasara a kansa

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.