BBC navigation

Abokan hamayya sun sa man ido: Inji Mancini

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:05 GMT
Manchester City

Roberto Mancini da Paul Lambert

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Roberto Mancini ya ce ya gaji da halayyar abokan hamayya bayan sabanin da suka samu da kocin Aston Villa watau Paul Lambert.

" Ban ce masa komai ba" a cewarsa. "Akwai wasu masu horas da yan wasa da ba sai ka ce masu uffan ba".

Mancini sun sami sabani da Lambert ne a karawar da suka yi inda Manchester City ta lalasa Aston Villa da ci 4-2 a gasar cin kofin Capital one.

Ko da yake Lambert bai dauki lamarin da zafi ba :" Ba komai. Idan abun da ya ce kenan. Mutum ne da na ke girmamawa a matsayin koci da kuma tsohon dan wasa."

Kocin Manchester City ya nuna fushinsa a wani hari da dan wasan tsakiya na Villa Joe Bennet ya kaiwa takwaransa na City Gareth Barry, abun da kuma ya sa suka musayar kalamai da Lambert.

" Na tambayi alkalin wasa ko zai bashi kartin gargadi ba tare da na daga hanu na ba , kwatsam sai ya zo wurina," a cewar Mancini.

" Na gaji da halayyarsu. A wasu lokutan masu horas da yan wasa na zuwa manyan filayen wasanni inda wani zai ce wani abu amma sauran ba zasu ce komai ba.

Kocin dan asalin kasar Italiya ya fuskanci lamari makamancin haka da takwaransa na Manchester United Sir Alex Ferguson, da ya zargi Mancini a matsayin mutumin da ya cika yiwa alkalan wasa surutu.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.