BBC navigation

Tshon kocin Norwich ya rasu

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 11:11 GMT

Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Norwich da Manchester City John Bond ya rasu yana mai shekaru sabain da tara a duniya.

A shekaru uku da ya shafe a matsayin kocin Man City, kungiyar ta samu damar karawa da kungiyar Tottenham a gasar FA cup ta karshe a shekarar 1981 inda suka sha kaye a hanun kungiyar ta Tottenham.

Marigayin ya kuma jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Norwich zuwa filin wasa na Wembley a shekarar 1975 a gasar cin kopin league ta karshe sai dai kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ita ce ta dauki kofin bayan ta doke Norwich da ci daya mai ban haushi.

John Bond ya buga kwallo har sau 381 a kungiyar kwallon kafa ta West Ham United tsakanin shekarun 1950 zuwa 1966

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.