BBC navigation

Lokacin Rio Ferdinand ya wuce, inji Shilton

An sabunta: 26 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 13:33 GMT
rio ferdinand

Rio Ferdinand

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila Peter Shilton ya bada shawarar da kada a sake gayyatar Rio Ferdinand ya bugawa kasar wasa saboda lokacinsa ya wuce.

Shilton ya furta hakan ne saboda rade-radin da ake yi cewa za a sake gayyato Rio Ferdinand kungiyar kwallon kafa ta kasar domin ya maye gurbin John Terry wanda ya sanar da ritayarsa daga bugawa Ingila kwallo a wannan mako kwana daya kafin ya gurfana a gaban kwamitin hukumar kwallon kafa ta Ingila kan zargin furta kalaman batanci da wariyar launin fata a kan dan uwan Ferdinand din Anton, zargin da wata kotu a baya ta wanke shi.

Peter Shilton wanda shi ne dan wasan da ya fi bugawa Ingila wasa a tarihi ya ce yana ganin bai kamata a sake dawo da Ferdinand ba domin a ganinsa ya kamata hangi gaba a nemo matasa.

Yana ganin kamata ya yi a dauki Gary Cahill na Chelsea da Joleon Lescott na Manchester City su rika bugawa Ingilan wasa a baya.

Daman tun a lokacin shirye shiryen zuwa gasar cin Kofin kasashen Turai ta 2012 da aka kammala kocin Ingilan Roy Hodgson bai dauki Ferdinand din ba mai shekaru 33 wanda kuma sau 81 yana bugawa Ingila wasa saboda abin da ya bayyana a lokacin dalilai na kwallon kafa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.