BBC navigation

Pulis na son FA ta bullo da doka mai tsanani

An sabunta: 27 ga Satumba, 2012 - An wallafa a 15:08 GMT
tony, pulis

Tony Pulis

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Stoke, Tony Pulis, ya bukaci Hukumar kwallon Kafa ta Ingila, FA, da ta bullo da wata doka ta haramtawa duk danwasan da aka samu da laifin faduwa da gangan domin samun bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida buga wasanni uku.

Pulis ya kawo wannan shawara ce saboda zargin da ya yi wa danwasan Chelsea na baya Branislav Ivanovic da faduwa da gangan a cikin da'irar yadi 18 ta Stoke City domin samun bugun-daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a wasan da kungiyoyin biyu su ka yi ranar Asabar wanda City ta sha kashi da ci 1-0.

A lokacin wasan alkalin wasan bai hukunta dan wasan na Chelsea ba duk da cewa ana ganin ya fadi ne da gan-gan amma kuma lokacin da dan wasan City din Oscar ya yi irin wannan laifi alkalin wasa ya hukunta shi inda ya bashi katin gargadi.

Kocin na Stoke City ya ce samar da wannan hukunci zai karfafawa 'yanwasa guiwa a kan su rinka kokarin nuna gaskiya a lokacin wasa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.